An Kashe Mutum 4 An Kona Bakuna A Kudancin Najeriya.

An kashe mutum uku tare da kona akalla bankuna hudu a rikicin karancin sabbin kudi a jihohin Oyo, Edo da Delta

 

An kashe mutum hudu ciki har da mace mai shayarwa, tare da kona akalla bankuna hudu a rikicin da ya barke kan karancin sabbin takardun kudi a Kudancin Najeriya.

 

Mai shayarwar ta rasu ne bayan harsashi ya same ta a wani ATM da take bin layin cirar kudi, sauran mutum ukun kuma sun rasu ne a rikicin da ya barke bayan masu neman sabbin kudi sun yi dafifi a Ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Jihar Edo.

 

Bankuna shida da suka hada da UBA, First Bank, Keystone, Access bank, Unity da Polaris na daga cikin wadanda masu boren suka farfasa wa tagogri tare da lalata musu ATM a jihar.

 

Aminiya ta gano cewa biyu daga cikin mamatan an kashe su ne a kan titin Akpakpava da ofishin na CBN yake, na ukun kuma ya gamu da ajalinsa ne a titin Sakpoba.

 

Ita macen ta hudu kuma harsashi ne ya same ta, amma ba ita jami’an tsaro suka nufa da harbin ba.

 

Rikicin ya barke ne bayan masu neman sabbin kudaden sun yi zargin wata mota da suke saton daga gidan gwamnati take ta nemi shiga harabar CBN din don neman sabbin kudi.

 

Sai mutanen suka ki amincewa, suka fara jifan ta, wanda hakan ya haifar da hatsaniya kafin daga bisani jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

 

Wani ganau ya rikicin ya kazance ne bayan wadanda da ke titin Sakpoba sun shiga cikin yamutsin, inda abin ya rikide zuwa kai fa bankuna da shaguna hari.

 

Aminiya

Spread to

Related Articles

Back to top button