An Naɗa Asuwaji Bola Tinibu mukamin Sarautar Gargajiya.

Shekaru kusan 17 da suka wuce Asiwaju Bola Tinubu ya zama Jagaban a masarautar Borgu

 

Marigayi Halliru Dantoro Kitoro III ya ba Gwamnan Jihar Legas wannan sarauta da ya zama Sarki

 

Halliru Dantoro Kitoro III ya hadu da ‘dan siyasar ne a lokacin da suka je majalisar dattawa a 1992

 

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta dauko salsala da tarihin zaman Asiwaju Bola Tinubu a matsayin Jagaban na masarautar kasar Borgu.

 

Marigayi Mai martaba Halliru Dantoro Kitoro III shi ne wanda ya ba Asiwaju Bola Tinubu wannan sarauta ta Jagaban a lokacin yana Sarkin Borgo.

 

A wajen nadin sarautar, mujallar City People ta rahoto Halliru Dantoro Kitoro III a shekarar 2006 yana bayanin dacewar Bola Tinubu da Jagaban.

 

A yayin da Basaraken ya ba Tinubu sarautar Jagaban, ya zabi Mai dakinsa, uwar gidar gwamnan Legas a lokacin (Remi Tinubu) ta zama Yun Bana.

 

Mai Borgu ya shaida cewa abokan takarsa da Gwamnan jihar Legas na lokacin ta yi tsawon shekaru 24, ta samo asali tun lokacin su na majalisa a 1992.

 

A jamhuriyya ta uku, Bola Tinubu da Halliru Dantoro Kitoro suka lashe zabe, suka zama Sanatoci a majalisar dattawa, kafin zuwan Janar Sani Abacha.

 

An zabi Tinubu ne a matsayin Sanatan yankin Legas ta yamma a jam’iyyar SDP, sai shi kuma Dantoro ya lashe zaben Arewacin Neja a karkashin NRC.

 

“Duk da ba mu jam’iyya daya, ni da Tinubu mun fahimci juna mun yi tarayya a harkokin kasa da-dama, sai mu da wasu ‘yan kishin kasa muka fara tafiya tare.

 

A cikin sauki sai muka samu kusanci da juna, amma ba mu san kasar mu za ta shiga mawuyacin yanayi ba. A 1993, Sani Abacha ya dawo da mulkin soja.

 

Mai martaban yake cewa shi da wasu Sanatoci 35 irinsu Tinubu, Chuba Okadigbo, Abu Ibrahim suka fara kalubalantar kifar da gwamnatin da soja suka yi.

 

Sarkin Borgu ya ce ya gano ‘dan siyasar yana iya sadaukar da ransa kan gaskiya, hakan ta sa da ya samu sarauta, ya tuna da abokin gwagwarmayarsa.

 

Vanguard ta ce sarautar Jagaban ta na nufin jagoran jarumai a kasar Arewa maso tsakiyar Najeriyan. An yi nadin sarautar a ranar 26 ga Fubrairu 2006.

 

A Oktoban 2015 Sarkin ya rasu, Tinubu yana cikin wadanda suka yi masa ganin karshe.

Spread to

Related Articles

Back to top button