Trending

Kotu ta dakatar da Gwamna wike Na Jahar Ribas.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal,
Jihar Ribas, ta haramta wa Gwamnatin Jihar
Ribas kamawa, muzgunawa da kuma tsoratar da
‘ya’yan jam’iyyar PDP na Dan kakarar shugaban
kasa Alhaji Atiku a jihar. Kotun ta
bayar da umarnin ne a ranar 19 ga watan Janairu
a karar da wani tsohon sanata a jihar Lee Maeba
da wasu mambobin jam’iyyar PDP da PCC su 13 a
jihar suka shigar kan gwamnatin jihar Rivers da
wasu mutum bakwai.
Sauran ‘ya’yan jam’iyyar
PDP da PCC da suka Sanya hannnu, sun hada da, daraktan yakin Neman zabe na jam’iyyar a jihar,
Abiye Sekibo da mai magana da yawunta, Leloonu Nwibubasa. Wadanda ake kara a karar
sun hada da Babban Lauyan Jihar Ribas, Sufeto
Janar na ‘Yan Sanda da Daraktan Hukumar Tsaro
ta Jihar.
Umurnin kotun ya bayyana a
wasu sassan kundin tsarin mulki da akayi anfani dasu: “sakin layi na Daya 1 zuwa na 8 da ya Hana tursasawa,
da tsoratarwa, da kamawa ko tsare wadanda suka shigar da karar bisa zargin karya, kaidodin da gangan,
shirya karairayi da yaudara ko karya Don musgunawa su masu karar, har zuwa lokacin gudanar da zabe.
saurare da kuma yanke
hukuncin a kan sanarwa.” Kakakin jam’iyyar PDP
PCC a jihar, Mista Nwibubasa, ya shaida wa
PREMIUM TIMES, a ranar Laraba, cewa, yanzu
haka magoya bayan Atiku Abubakar sun samu
kariya daga umarnin kotu bayan an gurfanar da
wasu daga cikinsu a gaban wata kotun majistare
a ranar Talata. Sama da mutum 20 daga cikin wadanda
aka gurfanar an tsare su a gidan yari, yayin da
aka dage sauraron karar wasun su zuwa ranar 22 ga watan Maris domin sauraron bukatar belinsu. Alhaji Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban
Najeriya ne, shi ne dan takarar shugaban kasa na
jam’iyyar PDP a zaben da za a yi a ranar 25 ga
watan Fabrairu.

Gwamna Nyesom Wike na
jihar Ribas ne ya bada umarnin kama magoya
bayan sa tare da gurfanar dasu a gaban kuliya.
Gwamna Wike a baya-bayan Nan sunyi ta Kai ruwa Rana, da shugabannin jam’iyyar PDP na
kasa bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa
Da aka gudanar na jam’iyyar a bara, ya Sha kayi a hannun
Atikun da ya zamo silar rikicin ba su. Gwamnan ya raba gari da PDP Ko shugabanninta bisa ga kin amincewa da alkawarin
da aka ce sunyi na tabbatar da korar Shugaban
jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu kamar yadda suka alkawarta, domin baiwa dan kudu
ya jagoranci jam’iyyar don tabbatar daidaiton
a jam’iyyar dama yankin.
Masari Atiku da Ayu duk
’yan Arewa ne. Ya zuwa yanzu dai Mista Wike ya
jagoranci Kungiyar G5, na gwamnonin PDP wadanda
Suke takun Saka da Alhaji Atiku da shugabancin
Jam’iyyar ta PDP a matakin kasa.

Sauran sun hada da Gwamna Samuel Ortom na jahar (Benue), dq Ifeanyi
Ugwuanyi na (Enugu), da Okezie Ikpaeazu na (Abia) sai Kuma Seyi Makinde na jahar Oyo, wadannan su ne mambobin G5 din.
Mambobin kungiyar da aka nada a kwamitin
yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku sun
janye mambobinsu tare da kauracewa taron
kaddamar da kungiyar.
Gwamna Wike a makon
da ya gabata ya soke amincewar da kotu tayi na
bai wa Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban
kasa na PDP na yin amfani da filin wasa na
Adokiye Amiesimaka wajen gangamin da zaa gudanar ranar 11
ga Fabrairu a jihar.

Spread to

Related Articles

Back to top button