Trending

Buhari Ya Amince Da Kafa Kwamitin Mutum 22 A Shirye-Shiryen Mika Mulki.

 

 

 

 

 

 

Sugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mutum 22 na Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar gwamnatin da za ta gaje shi daga ranar 29 Ga Mayu, 2023.

 

Daraktan Yaɗa Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, mai suna Willie Bassey, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

 

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha shi ne zai shugabanci kwamitin, wanda shi ne zai yi zaman tsara bayanin damƙa mulkin, domin tabbatar da an miƙa mulki cikin tsanaki daga gwamnati mai ci a yanzu da muka gwamnati mai hawa mulki daga ranar 29 Ga Mayu, 2023.

 

Sauran mambobin kwamitin sun sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Shari’a, sai wakilai daga Hukumar Babban Birnin Tarayya, FCT, Abuja, daga Maiakatar Ayyuka na Musamman, Fadar Shugaban Ƙasa da sauran su.

 

Mashawarcin Shugaban Ƙasa a Harkokin Tsaro, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Daraktan Hukumar Leƙen Asiri (NIA), Daraktan SSS sai kuma Rajistara na Kotun Ƙoli.

 

A ranar 14 Ga Fabrairu za a rantsar da su.

 

Tuni dai Buhari ya sanya wa doka hannu wadda ta ba shi damar kafa wannan kwamiti ya zama doka, ba tare da sai ya shawarci ko ya nemi amincewar Majalisa ba.

 

Daga cikin masu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 25 ga Fabrairu, guda huɗu ne ake ganin a cikin su ɗaya zai yi nasara a kan maye gurbin da Buhari zai sauka. Akwai Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.

Spread to

Related Articles

Back to top button