EPL: Mikel Arteta ya gaya wa Arsenal ta sayi dan wasan tsakiyar LaLiga.

 

Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya shaida wa kungiyar cewa ta sayi dan wasan tsakiya na Real Sociedad, mai shekara 24, Martin Zubimendi a kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara.
Zubimendi a shirye yake ya koma Arsenal a karshen kakar wasa ta bana, bayan da ya ki amincewa da komawar shugabannin gasar Premier a watan Janairu, saboda yana da sha’awar kammala kakar wasa da Real Sociedad.

Real Sociedad ta sanar da Arsenal cewa zubimendi na bukatar Yuro miliyan 60 na sakin zubimendi domin cinikin ya faru.

Spread to
Back to top button