Trending

Yakin Neman Karfin Fada Aji A Duniyar ‘Artificial Intelligence’ Ya Fara.

Kamfanin Google sun shigo duniyar ‘Artificial Intelligence’, yayin da a karon farko suka sanar da ‘AI’ din su na farko mai suna ‘DREAMIX’. A maimakon ChatGPT da yake baka amsar kusan duk abin abinda ka tambaye sa, Dell-E kuma yake baka hoton duk abinda zaka hakaito a kwakwalwarka ka.

 

Toh bari kuji shi kuma wannan sabon ‘AI’ din na Google me yake yi:

 

Idan ka saka masa hoton kowane abu, to zai mayar da wannan hoton daga hoto zuwa video. Bafa video na hoto ba, A’a video zai yi maka na gaske. Ina nufin ka dauki hoton Sunusi Danjuma Ali ka saka masa, to idan ka fadi me kake so ya maka da hoton zai dawo maka dashi a video.

 

Misali: A maimakon video da oga sunusi yake yi yanzu, sai ya siyi babbar waya da babbar camera, sannan ya zauna yayi editing na kwana biyu. Toh zai iya amfani da hoton shi kawai da ya dauka a daki mai kyau, yayi generating din duk kalar video din da yake so ba tare da yayi aikin sisi ba.

 

Sannan kuma wani abun gaba da mamaki da ‘Dreamix’ na kamfanin Google yake yi shine: Zaka iya rubuta masa gabaki daya script na labarin film, da kanshi zai maka generating film din da characters, tare da duk wani abun da kake tunanin akeyi a film. Kan Bala’i.

Banda ‘Dreamix’ akwai kuma ‘Bard AI’ shima duk Google suna kan yin aikin fitar dashi.

 

YADDA AI YAKE AIKI SHINE

 

Misali: Idan ina son na kirkiri AI wanda zai dinga tuqa mota, to ina da buqatar lallai sai na samu information da yawa game da yadda dan adam yake tuqa mota.

 

1. Ya mutane suke cin birki.

2. Ya ake yin kwana.

3. Me mutane suka fi haduwa dashi akan hanya idan suna tuqi.

4. Ta yaya mutane suke fahimtar abinda ya kamata su ciwa birki.

5. Ya mutane suke parking.

6. Me yake jawo hadari, kuma ya za’a kauce masa.

7. Ina ne hanya, ina ne ba hanya ba.

8. Taswira ‘Map’ na inda kake dss.

 

To bayan na samu biliyoyin wadannan informations din sai na dora su akan kwakwalwar software ta motar, daga nan idan ka kunna motar zata fara fahimtar da tazo guri gaza kwana zata yi, idan taga kaza birki zatayi dss.

 

To anan kuma kada fa mu manta Google yafi ko ina information a duniya, sune suke da fasahar Android, Gmail nasu ne, YouTube shima haka, Chrome ma haka. Kai kusan duk abinda muka fi amfani dasu a intanet mallakin Google ne.

 

Kamfanin Google yana da information da yawa game da mutane, Code din da aka rubuta program na Google ya kai layi Biliyan 2, mai bin sa MacOS ne da layi Miliyan 82, sai Facebook mai layi miliyan 62.

 

Hakanan Kamfanin Google da Apple da Facebook tare da Amazon su ne suka fi kowa yawan kudi cash a ajiye. Kai gwamnatin America ma tana rantar kudi a hannun Google. Sai dai kuma Masana suna cewa kamfanin OpenAI ya fitar da kaso 10% ne cikin darin abinda ChatGPT zai iya yi. Dama suna sane da Google zasu iya gasa dasu.

Muhammad Abdulrahman Sheka

Spread to
Back to top button