Wasiƙa zuwa ga Janar Murtala Mohammed.
Wannan wasiƙa ce da muka samu daga Mohammed Bala Garba Maiduguri, ɗalibi a Jami’ar Maiduguri kuma marubuci.
Babbar addu’ar da zan soma yi maka a wannan lokacin ita ce: Allah Ya kyautata makwancinka.
Da farko ina mai miƙa saƙon gaisuwa ta gare ka, da fatan kana cikin rahamar Ubangiji.
Bayan haka, kasantuwar yau (13/02/2023) kake cika shekara 47 da komawa wurin Mahaliccinka, ya sa na ga dacewar rubuta maka wannan wasiƙar.
Sai dai kash! Ban san ta inda zan fara bayyana maka abin da wasiƙar tawa ta ƙunsa ba saboda duk harsashin da ka dasa domin ganin mu ‘yan Arewa ba mu fuskanci wulaƙanci a rayuwa ba, an rusa su.
An wayi gari yau mu ne barace-barace a kan titi, shaye-shaye da yawon ɓata-gari, in ka ji jini ya zuba a ƙasa to mu-ya-mu ne. Yaƙi ya ci mu kuma ya ci iyayenmu, da mu da iyayen namu duk mun zama bayi.
Ba mu da hanyar bi ballatana wurin zuwa, kazalika mun rasa kuzarin tunkarar kowane irin ƙalubalen rayuwa.
Mutuwar zuciya duk ta cinye mu, ba ma cas ballatana as, sai zaman jiran ganima daga gwamnati, wanda kuma wannan babban kuskure ne.
Yau mun wayi gari da yawa daga cikinmu ba sa karatu sai yawon bangar siyasa.
Waɗanda suka yi karatun babu aikin yi, kuma babu makoma.
Ga iyayenmu ba su da abin yi, waɗanda suka yi aikin sai mutuwa suke ba fansho.
Yankinmu na Arewa yana neman zama kufai, ba a noma sai shuka gawawwaki, kullum muna cikin zullumi saboda babu kwanciyar hankali. Za ka zub da hawaye idan ka ga yadda muke rayuwa a yau.
Duk da Ubangiji Allah bai ja kwananka a kan karagar mulki ba, mun tabbata kai masoyinmu ne, matsayinka tabbatacce ne a cikin zukatanmu domin har yanzu akwai abubuwa masu rikitarwa game da abin da ka bari.
Ina burin zuwa birnin Kano domin kawai in shaƙi iskar mahaifarka inda ka tashi, na ziyarci kushewarka, na kai wa iyalanka da ‘yan uwanka ziyara, domin ji na nake tamkar wata tsoka daga gare ka.
Sai dai kash! Tsaron hanyarmu ta Maiduguri ya sa na yanke ƙauna daga yin hakan.
Nakan yi kukan zuci na yi hawaye a duk lokacin da na kalli hotonka a jikin takardar naira 20, sannan na ɗaga hannu na yi maka addu’a.
Zan yi matuƙar farin ciki idan ‘yan uwanka da iyalanka suka riski wannan wasiƙar tawa.
A ƙarshe ina yi maka fatan tabbata cikin rahamar Ubangiji tare da addu’ar Allah ya haɗa mu a gidan aminci (Aljanna).
Wassalam, daga masoyinka na har abada, Mohammed Bala Garba, Maiduguri.
BBC HAUSA
Saliadeen Sicey ✍️