Garin Ososo A Jihar Edo Najeriya.

Ososo Gari ne, da ke cikin ƙaramar hukumar Akoko-Edo , a arewacin jihar Edo, a Nijeriya. Yana da matsakaicin tsayin ƙafa 1236 sama da matakin teku, Yana da yanayi kamar na Jos , jihar Filato. Dutse Mafi girman kololuwa shine babban dutsen monolith wanda ake kira da Oruko rock.

Ososo Kuma kabila ce mai yawan jama’a kusan 200,108.

Garin Ososo yana da yanayi mai ban sha’awa, tare da wasu tuddai na asalin dutsen mai aman wuta masu dauke da duwatsu masu daraja.

Garin Ososo yana kan iyaka tsakanin jihohin Edo da Kogi, kuma a wani yanki mai tudu da duwatsu. Yana da tazarar kilomita 40 daga Igarra da kilomita 200 daga birnin Benin a jihar Edo.

Tarihi ya nuna cewa mutanen Ososo sunyi hijira ne daga Ogbe Quarter da ke cikin garin Benin a zamanin mulkin Oba Ozolua a shekara ta 1481 miladiyya, an kuma ce kakannin sun sha wahalhalu da yawa kuma sun sha asara mai yawa a kan hanyarsu ta zuwa Arewacin Najeriya. zuwa “IDA” wani gari a jihar Kogi ta yanzu su zauna na dan lokaci a wani wuri da ake kira ”Unuame” (bangaren ruwa) in da tafkin ya zo “Enidegbe”.

Mutanen Ososo sun kasa samun

kwanciyar hankali saboda yakin kabilanci shi ne yasa suka bar “Unuame” (gefen ruwa) bayan yakin shekara ta 1515 A:D sun samu matsa zuwa “Ososo’ in da suka sami kwanciyar hankali saboda rafi kuma ƙasa ce mai kyau don noma da farauta.

 

Saliadeen

Spread to
Back to top button