Trending

Tarihin Kafuwar Garin Mubi Dake Jahar Adamwa Atakaice.

 

WAIWAYE NE DOMIN ABAYA NA TABA BADA WANNAN TARIHIN

KASHI NA FARKO

Daga Dc Washington Mubi

Kafuwar garin Mubi ta samo asali ne ta wajen mutanen Lamurde..asalin sunan Mubi chanji ne daga Muvi zuwa Muyi lokacin musulunci bai zo kasar nan ba..Muvi wato Lamurde kenan itace komai domin acikin sarakunan lamurde 28 sarakuna guda 10 sukayi shugabanci akasan nan mutanen Lamurde ne kafin Musulunci tazo…Ta yadda musulunci yazo kamar yadda muka samu tarihi..zuwan musulunci anan mubi shine zuri’an su lamidon mubi na yanzu ..suka zo suka zauna da shanayensu adaji to idon mangariba yayi suna hura wa shanayensu wuta to mutanen Lamurde suna hangen wutan nan dake acikin daji da nisa..to shine Arnadon Lamurde na wanchan lokacin ya aika mutanensa suje su gano wani irin wuta ne yake ci acikin daji..mutanen Arnado suka je suka samu mutane ne da shanayensu acikin dajin daga nan sai mutanen Arnado suka dawo suka gayawa Arnado cewa mutane ne da shanayensu sai Arnado ya sake ya aika mutanen nasa wajen wayannan mutanen da shanayensu kuje Ku gayamusu inda suke zaunen nan sunyi nesa da mutane su maso kusa da mutane ..shine ainihin wayannan mutane da shanayensu wato zuri’an su lamidon mubi na yanzu suka taso daga cikin daji sukazo aka basu wurin zama agaya..Farkon zaman Fulani awannan gari na mubi shine gaya.to batun sunan mubi kuma anan ta samu ne saboda rashin iya kiran sunan Muvi shine Fulani suka sawa garin nan suna Muyi maimakon Muvi kenan..sannan Lamurde da kakeji ake kira Lamurde dashi don nan ne masarauta take..Shine suka chanja wanchan Muvi zuwa Muyi suka dauke Muvi zuwa Lamurde masarauta kenan.. lokacin da Fulani wato zuri’an su lamidon mubi na yanzu suka kusa da mutane da shanayensu suka gani fili bai wadace su ba..kasan bafulatane idon yana son chanjin wuri yana yawo don yaga wurin da yayi masa ya duba ya duba inda ya dace ya zauna shine suka bar Gaya zuwa Digil na yanzu ..da su ka zauna adigil ana nan Lamurde ta zaune amatsayinta na masaurata mubi kuma tana zaune amatsayin Muyin ta..to sai shi Usman Danfodio ya aiko ma sarkin Lamurde yaje ya karbu Addini wato Tutar Musulunci..shi Wanda aka aiko akan yaje ya karbo Tutar Musulunci wato Arnadon Lamurde sai yace shi bazai samu zuwa ba ya dauki mutuminsa daga cikin fadawansa ya hada da Malam Hamman wato zuri’an su Lamidon na yanzu Wanda suka taso daga cikin daji Wanda zuka dawo kusa dasu yace bafulatanin nan wato Malam Hamman yaje amaimakonsa ..to da sukaje sokoto anan Moddibo Adama ya rigasu isa sokoto to sai Shehu Usman Danfodio yace Moddibo Adama ya rigaku zuwa amma kuje kuyi zaman Amana..kai kuma Arnadon Lamurde mutanen da Allah ya hadaku dasu kuje kuyi zaman amana kuma karku ta basu karsu ta Baku sai shi Mallam Hamman ya dawo da tawagar da Arnado Lamurde ya turasu zuwa sokoto da ya dawo kasan darajan Musullunci wannan lokacin ne Arnadon Lamurde ya sauka daga kujeran sa ya bawa Mallam Hamman ya zama sarkin mubi..sarkin Lamurde yana karkashin sa..to da hakane ainihin kafuwar mubi..Ainihin sunan wannan garin ayaren Lamurde shine Muvi Wanda Fulani sukayi chanjinsa zuwa muyi wannan ta bangaren Fulani kenan.ana nan ana nan Hausawa sukazo su kuma dasu kazo amaimakon kiran Muyi nan basu iya ba sai suka maida shi Mubi kaga anan sunan Muvi ta koma Muyi sai na yanzu Mubi amma ainihin tushen kasan nan Lamurde ne Wanda Fulani suke kiranta Muyi Wanda hausawa sukace Mubi maimakon Muyi…..

Ku Biyo ni akashi na Biyu Kuji Kabilun Da ke akwai Agarin Mubi.

Spread to

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button