Matsalolin Dake Jawo Shafewar Tafin Hannu(Foot Drop)

Shanyewar tafin sawu, wato “foot drop” a turance, yana faruwa ne sakamakon shanyewar ko raunin jijiyar laka da ke kaiwa da komowar saƙonni zuwa ga tsokokin da suke da alhakin ɗago tafin sawu da yatsu sama .

Wannan matsala ta shanyewar tafin sawu na kawo matsala musamman yayin tafiya da sauran matsalolin da suke faruwa tare.

Abubuwan da ke kawo shanyewar tafin sawu sun haɗa da:

1) Lahani ko raunata jijiyar laka ta sharaɓa sakamakon matsalolin da ke biyo bayan tiyata, yanka, sara, suka ko haɗuran ababen-hawa, da sauransu.

2) Shanyewar ɓarin jiki

3) Cutar shan-inna

4) Kuskurewar allura a ɗuwawu, musamman ga ƙananan yara.

5) Shaƙewa ko danne jijiyar laka ta sharaɓa sakamakon:

a) ɗaurin karaya a ƙafa, musamman ɗorin karaya na gargajiya ko kuma idan ba a sami kulawa daga likitocin fisiyo tun daga farko ba.

b) danne tushen jijiyar lakar a gadon baya sakamakon ciwon baya.

c) doguwar naƙuda, musamman idan aka samu tsawaitar zangon naƙuda na biyu, da dai sauransu.

Alamomin shanyewar tafin sawu:

1) Kasa iya ɗago tafin sawu sama; wannan zai sa mutum ya ɗinga jan ƙafa ko tafin sawu. Saboda haka, masu wannan matsala su kan yi tintiɓe, da kuma samun wahalar riƙe takalmi a ƙafar har sai an sanya maɗaurin agara.

2) Ciwo a tsokokin sharaɓa, wato gaban sangalali ko ƙwauri zuwa tafin sawu.

3) Jin yanayi marar daɗi a sharaɓa, misali, ka ji kamar tafiyar kiyashi ko dindiris a sharaɓa zuwa tafin sawu.

Wannan matsala ana warkewa sarai kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya kawo nakasa a ƙafar. Saboda haka, akwai matuƙar buƙatar ganin likitocin fisiyo domin sune ke kula da farfaɗo da aikin jijiyar laka da tsokokin har aikinsu ya dawo yadda ya kamata.

#FootDrop
#DroppedFoot
#InjectionPalsy
#ObstetricPalsy
#LowBackPain

©Physiotherapy Hausa

Spread to

Related Articles

Back to top button